Catalonia: Masu Neman Ballewa Sun Lashe Zaben Majalisar Dokoki
Jam'iyyun da suke goyon bayan 'yancin yankin Catalonia na kasar Spain sun sami nasara a zaben 'yan Majalisar dokokin da aka yi a yanki da kujeru 70 a jumillar 135.
An rusa tsohuwar majalisar wacce ita ma masu son ballewar suke da rinjaye a cikinta.
Tsohon shugaban majalisar dokokin, Carles Puigdemont wanda jam'iyyarsa tana cikin wadanda suka sami nasara, ya bukaci ganin an wanke shi daga tuhumar da aka yi masa a baya.
A halin da ake ciki Puigdemont yana zaman hijira a kasar Belgium, ya kuma bukaci ganin an saki wasu jami'an gwamnatin yankin na catalonia da ake tsare da su a cikin kasar ta Spain.
Yankin na Catalonia wanda yake arewa maso gabacin kasar Spain ya dade yana fafutukar samun 'yanci daga kasar.