Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Zama Kan Kasar Iran
A daren Jiya Juma'a ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara gudanar da zama na tattaunawa kan hatsaniyar baya bayan nan da ta faru a kasar Iran.
Wannan zama dai na zuwa ne bisa bukatar kasar Amurka, kafin fara zaman, kasar Rasha ta bukaci a gudanar da zaman sirri domin a gano cewa mafi yawa daga cikin mambobin kwamitin ne ke bukatar a gudanar da wannan zama? sai dai a yayin zaman, Amurka ta yi amfani da karfi wajen matsin lamba ga wasu kasashe inda ta samu rinjaye da kashi 9 cikin 15, da hakan ya bayar da damar gudanar da zaman a bayyane.
Nikki Haley wakiliyar Amurka a MDD ta bayyana cewa kasar ta za ta goyi bayan wadanda suka tayar da hatsaniya a kasar Iran.
A yayin zaman, wakilin kasar Bolivia a MDD ya tabbatar da cewa kasar Amurka ta mayar da kwamitin tsaon MDD wani makami na siyasa, domin a ganin sa hatsaniyar da ta faru a kasar Iran ba ta da alaka da batun da ya kamata a tattauna ta a kwamitin tsaron MDD, abu ne da ya shafi harakokin cikin gidan kasar Iran.
kafin hakan dai, Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya zargi Amurka da yin katsa landan ga harakokin cikin gida na kasar Iran tare da cewa Amurkan ta mayar da zauren MDD a matsayin wani makami na cimma manofinta na siyasa.