Kungiyoyin Ta'addancin Takfiriyya Da Hidimar Da Suke Yi Wa H.K. Isra'ila
(last modified Sat, 27 Jan 2018 05:54:44 GMT )
Jan 27, 2018 05:54 UTC
  • Kungiyoyin Ta'addancin Takfiriyya Da Hidimar Da Suke Yi Wa H.K. Isra'ila

Cikin 'yan kwanakin nan dai kafafen watsa labarai daban-daban suna ci gaba da karin bayani dangane da sabuwar alaka da aiki tare da ke tsakanin haramtacciyar kasar Isra'ila da kungiyoyin ta'addancin 'yan takfiriyya a kasar Siriya bayan da 'Isra'ila' ta kafa wata sabuwar kungiyar ta'addanci a yankin tuddan Golan na kasar Siriya da take mamaye da shi.

Cikin wani rahoto da ta watsa, kafar watsa labaran 'The Intercept" ta Amurka, ta bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila ta kafa wata kungiya da ta kira 'yan sandan kan iyaka da ta kumshi kungiyoyin 'yan ta'addan takfiriyya da suke kudancin kasar Siriya da nufin ba da kariya  ga kan iyakokin yankin Golan da yahudawan suka mamaye. Tsawon wannan rikici na kasar Siriya, sahyoniyawan sun kasance masu ba da taimako ta bangarori daban-daban ga kungiyoyin ta'addancin da suke yankin da suka hada da ba su makamai da bayanan sirri bugu da kari kan ba da magani da kulawa ta likitanci ga wadanda aka raunana daga cikinsu.

Rahotannin da aka fitar dangane da kokarin da sahyoniyawan suke yi wajen tabbatar da iko da kuma mamayarsu suna nuni da cewa haramtacciyar kasar Isra'ila tana kokarin tabbatar da ikonta ne tun daga tuddan na Golan da ta mamaye har zuwa lardunan Quneitra da Dar'ah na kasar Siriyan, wanda hakan yana nufin tabbatar da ikonsu na tsawon kilomita 40 wajen yankin Golan din da ta mamaye; kamar yadda kuma suke son su yi tarayya da kungiyoyin 'yan ta'addan da suke rike da wadannan yankuna wajen gudanar da su. 

Tun a tsakiyar shekarar bara (2017) ce dai gwamnatin 'Isra'ilan' ta fara gudanar da bangare na biyu na wannan shiri nata yayin da sojojin da kungiyoyin leken asirin haramtacciyar kasar suka fara ba da horo da ba da makamai ga wasu dakarun da suka kai mutane 500 da aka ba su sunan "Liwa Forsan al Joulan" (Golan Knight) ko kuma 'Jaruman Golan" wanda babban aikinsu shi ne sanya ido da kuma kare wadannan kan iyakoki da kuma gabatar da rahoto a kai a kai wa haramtacciyar kasar Isra'ilan.

Rahotanni daban-daban dai suna nuni da irin alaka ta kut da kut da take tsakanin kungiyoyin takfiyyan kasar Siriya da haramtacciyar kasar Isra'ilan, wanda hakan a sannu a hankali na tabbatar da gaskiyar ikirarin jami'an kasar Siriyan na cewa suna fada ne da kungiyoyin ta'addanci daban-daban da suke samun goyon baya da taimakon Amurka, kasashen Yammaci, wasu na larabawa musamman Saudiyya da kuma Haramtacciyar kasar Isra'ila duk dai da nufin ganin bayan gwamnatin Siriya da kuma tabbatar da iko da kwanciyar hankalin haramtacciyar kasar Isra'ilan.

A baya bayan nan jaridar Al-Quds al-Arabi, ta buga wata makala da sanannen marubucin nan dan kasar Palastinu Muhammad Ayash ya rubuta cewa: Tun bayan harin 11 ga watan Satumba, Isra'ila ta kasance tana amfani da hare-haren ta'addancin da suke faruwa a duniya wajen cimma manufofinta, wato a takaice dai Isra'ila tana daukar hare-haren ta'addancin da ake kai wa a matsayin wata dama da ta samu wajen ciyar da manufofinta gaba.

Masana harkokin yau da kullum na yankin Gabas ta tsakiya sun yi amanna da cewa kungiyoyin ta'addancin da suke yankin Gabas ta tsakiya, idan ba don goyon baya da taimako na makamai da suke samu daga kasashen waje ciki kuwa har da haramtacciyar kasar Isra'ila, to da kuwa ba su yi irin karfin da suka yi da kuma aikata irin munanan ayyukan da suka aikata ba. Ko shakka babu tsawon shekarun baya-bayan nan 'Isra'i'a' ta hanyar goyon bayan Amurka tana ci gaba da amfani da kungiyoyin 'yan ta'adda wajen haifar da fitina da rikice-rikice a yankin Gabas ta tsakiya da kuma raunana kasashen yankin, bugu da kari kan mayar da batun mamayar da ta yi wa Palastinu a matsayin wani lamari na bayan fage, wanda hakan zai ba ta damar cimma bakar aniyar da take da shi na ta mamaya da kuma tabbatar da ikonta a kan kasashen larabawa musamman kasar Siriya.