MDD Ta Bukaci Taimakon Kudi Ga 'Yan Gudun Hijrar Boko Haram
(last modified Wed, 31 Jan 2018 18:03:30 GMT )
Jan 31, 2018 18:03 UTC
  • MDD Ta Bukaci Taimakon Kudi Ga 'Yan Gudun Hijrar Boko Haram

Babban Kwamishinan dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya bukaci taimakon kudi na dala miliyan 160 domin taimakawa 'yan gudun hijrar da rikicin boko haram ya raba da gidajensu a yankin tabkin Chadi.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto babban kwamishin dake kula da 'yan gudun hijra cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba ya ce Majalisar dinkin Duniya da abokanin aikinta na taimakon gagguwa ya zama wajibi a gare su, su biya bukatun 'yan gudun hijrar Niajeriya dubu 208, da kuma wasu dubu 75 da aka karbi bakuncinsu a jamhoriyar Nijer, Kamaru da Chadi.

Cikin bayanin da Majalisar ta fitar ta tabbatar da cewa har yanzu akwai 'yan gudun hijrar Najeriya dake rayuwa a tsakanin al'umma a cikin kasashe makwabta.

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra na MDD ya sake  kira kungiyoyin kasa da kasa da su zuba taimakon dala miliyan 241 da suka yi alkawarin bayarwa a shekarar 2017 din da ta gabata, da hakan zai cike gurbin kashin 56% na kasafin kudin kwamitin.

Bisa kididdigar MDD, sama da mutane dubu 20 ne rikicin boko haram ya raba da mahalinsu a kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru Chadi daga shekarar 2009 zuwa yanzu.