Kungiyar ISIS ta dauki nauyin kai harin Brussels
-
harin Belgium
Kungiyar 'yan ta'adan ISIS ta dauki nauyin kai harin Brussels da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 30 tare da raunana wasu sama da 200 a wannan Talata.
kungiyar dai ta dau alhakin kai harin ne a wata sanarwa da harsunan larabci da faransanci a shafin internet inda kuma tayi alkawarin ci gaba da kai wasu hare-hare nan gaba.
Harin dai na farko an kai shi ne a filin jirgin sama na Zaventem, sai kuma na biyu bayan sa'a guda da aka kai a tashar jirgin kasa ta Malbeek da ke birnin na Brussels.
Kamfanin dillancin labarai na kasar ya rawaito cewa, sai da aka fara jin karar harbe harben bindiga tare jin muryar wasu mutane da ke magana a harshen Larabci kafin a samu fashewar abubuwan guda biyu a filin jirgin saman da kuma daya a tashar jingin kasa.
Tuni kasar ta Belgium dama kasashen Turai da dama suka tsaurara matakan tsaro, yayin da sauran kasashen duniya ke ci gaba da yin allawadai da wadanan hare-haren.