An Dakile Yunkurin Harin Ta'addanci Biyu A Faransa
(last modified Sun, 25 Feb 2018 10:51:09 GMT )
Feb 25, 2018 10:51 UTC
  • An Dakile Yunkurin Harin Ta'addanci Biyu A Faransa

Mukumomi a Faransa sun sanar dakile harin ta'addancin biyu tun daga watan Janairu da ya gabata zuwa yanzu.

Ministan cikin gida na kasar, Gérard Collomb wanda ya sanar da hakan a tashar talabijin ta Europa 1, ya ce, an shirya kai hare haren a wurin wassanin motsa jiki da kuma kan sojojin kasar.

Tuni dai aka cafke mutanen da suka shirya kai hare-haren kuma za'a musu shari'a nan gaba, tare kuma da rufe wasu masallatai uku a kudu maso gabashin kasar da kuma Paris, saboda yada tsatsaran ra'ayi.

Al'kalumman da hukumomin kasar suka fitar sun nuna cewa tun daga shekara 2017 data gabata an dakile jerin hare-hare masu nasaba da ta'addanci 20 a kasar ta Faransa.