Amurka Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Yaki Da Ta'addanci
Mar 13, 2018 05:52 UTC
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce Kasarsa za ta ci gaba da tallafawa Najeriya a fanonin da suka shafi yaki da ta'addanci dama ababen more rayuwa.
Tillerson wanda ke sanar da hakan yayin ganawarsa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari a ziyarar da ya kai jiya a Nahiyar ya ce a shirye Amurka take ta kara karfafa alaka da Najeriyar.
Sakataren harkokin wajen Amurkar ya shafe sa’o’I kadan a Najeriyar kafin koma birnin Washington, a ran gadin da ya kaddamar a Afrika wacce ya karkara daga Najeriya.
Ana bayyana ziyarar ta Tillerson dai da nufin wanke cin mutuncin da shugaba Donald Trump na Amurkar ya yi ga Nahiyar ta Afrika dama shuwagabanninta.
Tags