Iran Ga Saudiyya: Duniya Ta San Wake Goyon Bayan 'Yan Ta'adda
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar da kalaman ministan harkokin wajen Saudiyya inda ya zargin Iran din da goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya, tana mai cewa duniya dai ta san waye mai goyon bayan kungiyoyin ta'addanci a duniya.
Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Iran Bahram Qassemi ya bayyana hakan inda ya ce: A yau dai ba abu ne da ya buya ga kowa ba, cewa wace kasa ce sannan kuma wace akida ce ta ke yada ta'addanci, rashin tsaro, tsaurin ra'ayi da rashin tabbas a yankin Gabas ta tsakiya da kuma duniya baki daya, yana mai ishara da akidar wahabiyanci wanda Saudiyya take yadawa a matsayin tushen dukkannin wadannan ayyukan ta'addancin da ke faruwa.
Har ila yau kakain Ma'aikatar harkokin wajen na Iran yayi ishara da irin tsayin dakan da Iran ta yi wajen fada da wadannan ayyukan ta'addancin da Saudiyya da kawayenta suke yadawa a yankin Gabas ta tsakiya ta hanyar amfani da dukiya da kuma goyon bayan da take samu daga Amurka inda ya ce ministan harkokin wajen na Saudiyya ba shi da bakin da zargi wani da goyon bayan ta'addanci da yada rashin tsaro a yankin Gabas ta tsakiya alhali kuwa shi ne kan gaba wajen goyon bayan kisan gillan da ake yi wa al'ummar Yemen.
A jawabin da yayi ne a Washington, Ministan harkokin wajen Saudiyyan Adel al-Jubeir ya bayyana Iran a matsayin babbar matsalar sannan kuma tushen goyon bayan ayyukan ta'addanci da kuma tsaurin ra'ayi.