Da Makaman Faransa Saudiyya Ke Kai Farmaki A Yemen_ Kungiyoyi
(last modified Thu, 29 Mar 2018 16:19:01 GMT )
Mar 29, 2018 16:19 UTC
  • Da Makaman Faransa Saudiyya Ke Kai Farmaki A Yemen_ Kungiyoyi

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da dama sun ce, shekaru uku na hare haren da Saudiyya ke jagoranta a Yemen, ana kai su ne da makaman yaki da Faransa ta sayar wa Saudiyya.

Kungiyoyin sun ce hare haren sun shafi makarantu, asibitoci da kuma gidajen fararen hula a kasar ta Yemen, wanda ya hadassa hasaren rayukan mutane kimanin 10,000 da jefa kasar cikin matsananciyar yinwa.

Wannan dai a cewar kungiyoyin zai ci gaba muddin majalisar tarayya turai taba bukaci kakaba takunkumi kan mika wa Saudiyya makamai ba.

A karon farko da yake tabbatar da mikawa Saudiyya makaman yaki, ministan harkokin wajen faransa, Jean-Yves Le Drian, a wata hira da gidan radiyon RTL, ya ce suna mutunta dokokin kasa da kasa da kuma yin taka tsatsan wajen mikawa Saudiyya makamai. 

Binciken da cibiyar YouGov ta gudanar ya nuna cewa kashi 74% na Faransawa na kyamar sayar wa Saudiya makaman yaki da kayayyakin aikin soja, sannan kashi 71% na Faransawan kuma, ba sa kaunar sayar wa Daular Larabawa da sauran kasashen kawancen da ke yaki a Yemen makamai.

Alkalumman da MDD ta fitar sun nuna cewa, a cikin shekaru uku da Saudiyya ta kwashe tana jagorantar kai farmaki a Yemen, an shiga wani bala'i mafi tsanani a kasar ta Yemen, wanda shi ne mafi muni a halin a doron duniya nan, inda mutane kimanin sama da miliyan 22 ke bukatar agaji.