Rasha Ta Kori Jami'an Diflomatsiyan Amurka 60
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29474-rasha_ta_kori_jami'an_diflomatsiyan_amurka_60
Kasar Rasha ta kori jami'an diflomatsiyan Amurka guda 60, da kuma rufe karamin ofishin jakadancin Amurkar na birnin Saint-Pétersbourg, a mastayin maida martani kan korar nata jami'an da Amurkar ta yi biyo bayan zargin yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan da 'yarsa a Birtaniya.
(last modified 2018-08-22T11:31:37+00:00 )
Mar 29, 2018 18:21 UTC
  • Rasha Ta Kori Jami'an Diflomatsiyan Amurka 60

Kasar Rasha ta kori jami'an diflomatsiyan Amurka guda 60, da kuma rufe karamin ofishin jakadancin Amurkar na birnin Saint-Pétersbourg, a mastayin maida martani kan korar nata jami'an da Amurkar ta yi biyo bayan zargin yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan da 'yarsa a Birtaniya.

Da yake sanar da matakin a yau Alhamis, ministan harkokin wajen Rashar ya ce wannan martanin kasarsa ne ga Amurka akan matakin korar jami'an Rashar su 60.

Game da sauren kasashen da suma suka kori jami'an Rashar, Mista Lavrov ya ce kasarsa zata dau mataki daidai irin wanda suka dauka.

A lokacin da yake sanar da matakin, Mista Lavrov ya ce tuni  suka kira jakadan Amurka, don sanar dashi matakin maida martani na Rashar, ga Amurka.

Dama kafin hakan Rasha ta sha alwashin mayar da kakkausan martani kan matakin da kasashe fiye da 20 suka dauka na korar jami'an diflomasiyyarta kimanin 140, don nuna goyan bayan Biritaniya akan zargin yunkurin kashe wani tsohon jami'in leken asirin Rashan mai suna Sergueï Skripal da batun ta tada kura sosai da kuma janyo takaddamar diflomatsiya tsakanin Rasha da kasashen Turai.

Rasha dai na ci gaba da musunta hannun a yunkurin kisan jami'in, tare da zargin Biritaniya da kin bada hadin kai don gudanar da bincike.