Isra'ila Ta Soke Yarjejeniyar Bakin Haure Da MDD
(last modified Tue, 03 Apr 2018 11:10:12 GMT )
Apr 03, 2018 11:10 UTC
  • Isra'ila Ta Soke Yarjejeniyar Bakin Haure Da MDD

Firayi Ministan yahudawan mamaya na Israila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da soke yarjejeniyar bada izinin zama ga bakin haure 'yan Afrika.

Mahukuntan yahudawan sun sanar da yammacin jiya cewa sun dakatar da yarjejeniyar da suka cimma da 'yan sa'o'i kadan da MDD, don mayar da bakin hauren dake zaune Isra'ilar ba bisa ka'ida ba zuwa wasu kasashen da suka ci gaba.

Dama kafin hakan yarjejeniyar da Netanyahu ya sanar ta zo wa da kasashen da aka ce za'a tisa keyar bakin hauren da mamaki.

Ministan harkokin wajen Italiya, wanda ya fara tsokaci kan batun, ya ce babu wata yarjejeniya da kasarsa ta cimma a shirin na Isra'ila da hukumar kula da bakin haure ta MDD donkarbar bakin haure.

A Jamus ma batun ya so yin kama da hakan, inda ministan cikin gida na kasar ya ce ba shi da wata masaniya kan shirin.