Amurka Ta Amince Da Sayarwa Saudiya Makamai
(last modified Fri, 06 Apr 2018 06:31:06 GMT )
Apr 06, 2018 06:31 UTC
  • Amurka Ta Amince Da Sayarwa Saudiya Makamai

Hukumomin Amurka sun amince da bukatar kasar Saudiya na sayar mata da makamai na dala bilyan 1.31.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto ma'aikatar wajen Amurka a jiya alhamis na cewa shakka babu za mu sayarwa da kasar Saudiya makamai matukar dai Majalisar dattijan kasar ta amince, a yanzu majalisar datijan kasar ta Amurka nada wa'adin kwanaki 30 na amincewa ko watsi da wannan bukata.

Ko a kwakin baya, ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta sanar da amincewarta na sayerwa kasar Saudiya makamai da suka hada da makamai masu linzani dubu 6 da da dari shida na tsabar kudi bilyan guda na dalar Amurka.

A shekarar da ta gabata, shugaba Trump na Amurka ya ziyarci birnin Riyad na Saudiya, inda a wancan lokacin ya sanar da cewa kasar sa za ta sayerwa da saudiya makamai na dala biliyan 110.

A ziyarar baya-bayan nan da ya kai Amurka, Shugaba Trump ya bukaci Muhamad bn Salman yariman kasar Saudiya mai jiran gado da kara yawan makaman da yake saye daga Amurka.