Amurka: Shugaban Ma'aikatan Fadar White House Ya Yi Barazanar Barin Aikinsa
(last modified Sun, 08 Apr 2018 06:34:52 GMT )
Apr 08, 2018 06:34 UTC
  • Amurka: Shugaban Ma'aikatan Fadar White House Ya Yi Barazanar Barin Aikinsa

Rahotanni daga Amurka na cewa, sakamakon kai ruwa rana da ake yi tsakanin shugaban kasar Amurka da John Kelly shugaban ma'aikatan fadar White House, hakan ya sanya John Kelly din yin barazanar ajiye aikinsa.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, sakamakon cin zarafin da Trump ya yi wa shugaban ma'aikatan fadar White House a wani zama da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris da ya gabata, bayan dawowarsa hotu a jiya, John Kelly dan shekaru 67, ya yi barazanar cewa zai daina aiki a karkashin gwamnatin Trump.

Daga watan Janairun 2017 da Trump ya shiga fadar White House ya zuwa yanzu, fiye da manyan jami'an gwamnatinsa 20 ne suka yi murabus, mafi yawa daga cikinsu suna bayyana shi da cewa mutum ne mai girman kai da bai san aiki ba, wanda kuma baya daukar shawara.

A cikin 'yan kwanakin nan ne Trump ya sauke sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Rex Tillerson daga kan mukaminsa, sakamakon sabanin da ke tsakaninsu.