Brussels : An Bukaci Al'umma Su Kauracewa Ganggami
-
wasu dake juyayin harin Brussels
Hukumomin a Belgium sun kirayi al'ummar kasar dasu kauracewa gangamin da aka shirya yi ranar Lahadi a Brussels saboda barazana tsaro dama yiwuwar kai wasu sabin hare-haren ta'andanci.
An dai shirya yin gangamin ne domin yin allawadai da hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane 31 ran Talata data gabata.
Hukumomin kasar dai sun ce ganin yadda har yanzu babu tabas akan yanayin tsaro dama yadda ake ci gaba da bincike kan hare-haren da suka girgiza kasar suna kira ga al'ummar kasar da kada su halarci gangamin na gobe.
Da yake bayana hakan a wani taron manema labarai, maganin birnin Brussels Yvan Mayeur ya bukaci jama'ar dasu jinkirta gangamin nasu har zuwa makwani masu zuwa, wanda zai baiwa masu bincike gundanar da aikin su cikin sanaki.
Dama kafin hakan shi ma ministan cikin gina na kasar ya shawarci al'umma kasar dasu kauracewa gangamin saboda barazana ta'adanci.
A halin da ake ciki dai masu gabatar da kara na Belgium din wadanda ke binciken harin kunar bakin wake Brussels sun tuhumi wani mutum da aka bayyana da sunan Faycal C da aikata kisan ta'addanci.