MDD Ta Sake Jaddada Muhimmancin Mutunta Yerjejeniyar Nukliyar Kasar Iran
Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Antonio Guteres, a wani taron da ya halatta a birnin Swizland a jiya Lahadi ya kara jaddada muhimmancin mutunta yerjejeniyar da kasar Iran ta cimma da manya manyan kasashen duniya kan shirinta na makamashin Nukliya.
Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Guteres yana cewa an samar da yerjejeniyar ce don tabbatar da zaman lafiya a duniya don haka bai kamata a yi watsi da ita ba.
A ranar 22 ga watan Maris da ta gabata ma shuwagabannin wasu kasashen Turai, wadanda suka hada da na Faransa da Jamus sun kara jaddada goyon bayansum ga wannan yerjejeniyar duk tare da dagewar gwamnatin kasar Amurka kan cewa sai an yi mata koskorima, wanda zai hada da takaita makaman masu linzami na kasar Iran.
Har'ila yau Federica Mogherini jami'a mai kula da harkokin kasashen waje na tarayyar Turai, ita ma ta kara jaddada kan cewa yerjejeniyar ta kasa da kasa ce don haka akwai muhimmancin a kiyayeta.
Kasar Amurka dai ta yi baraznar ficewa daga yerjejeniar idon har sauran kasashen da aka kulla yerjejeniyar da su sun ki amincewa da yi mata koskorima.