Faransa : Macron Na Ziyara A Amurka
Yau Litini, shugaba Emanuelle Macron na Faransa ke fara ziyara a Amurka, mai manufar shawo kan takwaransa na Amurkar ya canza ra'ayinsa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, ta ci gaba da aiki.
Gabannin zuwansa a Washington, Mista Macron ya bayyana a wata hira da tashar talabijin ta FOX a birnin Paris cewa, "tilas mu sake gina Syria bayan yakin, tare da jaddada cewa bin hanyar siyasa ita ce mafi dacewa.
Shugaba Trump yace yana son ya janye sojojin amurka daga Siriya nan bada jimawa ba, sannan ya yi barazanar janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran, inda ya baiwa kasashen Turai wa'adin har zuwa 12 ga watan Mayu na su canza fasalin yarjejeniyar.
Ziyarar T aMcron na zuwa 'yan kwanaki kadan bayan harin saman soji da kasashen Amurkar da Biritaniya da kuma Faransar suka kai Siriya kan zargin amfani da makami mai guba a yankin Duma.