Rasha : Ana Shirin Rantsar Da Putin A Wa'adin Mulki Na Hudu
A Rasha, yau Litine ce shugaban kasar, Vladimir Putin, zai yi ratsuwar kama aiki a wa'adin mulki na hudu, wanda zai bashi damar ci gaba da shugabancin kasar har zuwa shakara 2024.
A watan Maris da ya gabata ne Mista Putin, ya lashe zaben shugabancin kasar da kashi 76 cikin dari na yawan kuri'un da aka kada, wanda kuma shi ne zabe mafi rinjaye da aka masa tun bayan hawansa kan karagar mulki.
Kafin hakan dai shugaba Putin ya shafe shekaru 18 yana kan madafin ikon kasar ta Rasha.
Bayan sake zaben da aka masa a watan na Maris, da yake amsa tambayar cewa, ko bayan wannan wa'adin zai sake tsayawa takara, Shugaba Putin ya masa cewa '' kuna tsammanin zan tsaya har in cika shekara 100'' A'a.
Idan dai har ba kwaskwarima aka wa kundin tsarin mulkin kasar ba, Shugaba Putin bai da damar sake tsayawa takara a 2024.