MDD:Kawo Karshen Boko Haram Yana Bukatar Lokaci.
Wakilin MDD na musamman a Yammacin Afirka ya bayyana cewa kawo karshen kungiyar ta'addancin boko haram na bukatar lokaci na wasu shekaru duk kuwa da cewa an karya lagon kungiyar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Wakilin MDD na musamman a Yammacin Afirka, Mohamed Ibn Chambas yayin da yake halartar taron yankin tabkin Tchadi da ya gudana a birnin Maiduguri na shiyar arewa maso gabashin Najeriya ya ce kungiyar Boko haram ta zamanto wani sashe na kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya kuma kawo karshen gaba daya na bukatar lokaci na wasu shekaru.
A yayin da yake halartar taron kasashen yankin tabkin Chadi da suka hada da (Nigeria, Niger, Tchadi da Kamaru) Mohamed Ibn Chambas ya yi alawadai kan hare-haren da kungiyar Boko haram ke ci gaba da kaiwa a wasu yankunan Nigeria, musaman ma a jahorin Yobe da Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar.
Daga shekarar 2009 zuwa yanzu hare-haren kungiyar boko haram ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu 20 da kuma raba wasu sama da miliyan biyu da dubu 600 da mahalinsu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.