An kame Mutane Uku kan zarkin ta'addanci a kasar Belgium
Kotu a kasar Belgium ta bada umarnin kame wasu mutane guda Uku da ake zarkin su nada hannu wajen aiyukan ta'addanci a kasar
A yau Litinin ne kotun ta bada umarni da a tsare Yassine A, Mohamed B da Aboubaker O kan zarkinsu da alaka tare da wata kungiyar 'yan ta'adda, saidai kotun ba ta bada cikekken bayyani ba kan cewa wadannan mutane uku da aka kame suna hanu a harin ta'addancin da aka kaiwa filin jiragen sama da tashar jirgin kasa na birnin Brussels a ranar talatar da ta gabata.
A bagare guda kuma mahukuntan kasar sun bayyana cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu sandaiyar harin ta'addancin da aka kai birnin Brusseles ya haura zuwa 35, kuma daga cikin mutane 340 din da suka jikkata, har yanzu a kwai mutane 101 dake kwance a gadajen Asibiti.
Tun bayan harin ta'addancin da aka kai birnin Faris na kasar Faransa a watan Nuwambar shekarar 2015 din da ta gabata, Kungiyar ISiS ta yi barazanar kai irinsa a kasar Belgium, inda a ranar talata 22 ga watan Maris din nan ta tabbatar da hakan a aikace inda ta kai wasu tagwayen hare-haren a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Brussels da kuma tashar jirgin kasansa.