Kwamitin Tsaron MDD Ya Gudanar Da Zama Kan Falastinu
Taron gaggauwa da kwamitin tsaron MDD ya kira kan Falastinu ya watse ba tare da fitar da sakamako ba.
A daren jiya talata ce, kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron gaggauwa kan ta'asar da Isla'ila ta aikata kan falastinawa, inda mafi yawa daga cikin manbobin kwamitin suka bukaci a gudanar da bincike kan kisan gillar da jami'an tsaron HKI suka yi Falastinawa, kuma a wannan laraba ce ake sa ran za rubuta wannan kuduri a kwamitin.
A nasa bangare, Nikolay Mladenov manzon MDD zuwa yankin gabas ta tsakiya ya bukaci mahukuntan Isra'ila da na Masar da su bayar da damar fitar da wadanda suka jikkata daga yankin Gaza.
Da dama daga cikin mahalarta taron ciki har da wakilin kasar Kuweit a zauren MDD sun yi alawadai da kisan kiyashin da jami'an tsaron HKI suka yiwa Palastinawa a ranar Litinin din da ta gabata tare da bayyana hakan a matsayin take hakkokin kasa da kasa,
Saidai a nata bangare, Nicky Haley wakiliyar Amurka a zauren MDD ta nuna goyon bayanta ga Isra'ila tare da dora laifin kan kungiyar Hamas.
A ranar Litinin din da ta gabata, Sojojin yahudawa sahayoniya sun kashe falasdinawa sama da 60 a zirin Gaza, a zanga zanga da falastinawan ke yi kan mayar da Kudus babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.