Amurka Na Ci Gaba Da Kakaba Wa Iran Takunkumi
A ci gaba da takunkumin da take kakabawa kasar Iran, baitul malin kasar Amurka ta sake sanya takunkumi kan wani kamfani da jami'an kasar ta Iran.
Wannan dai shi ne takunkubi na biyu da kasar Amurka ta kakabawa jamhiroyar musulinci ta Iran, tun bayan da ta fice daga yarjejjeniyar nukiliyar zaman lafiya na Iran tare da manyan kasashen duniya biyar gami da kasar Jamus.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin baitul-malin kasar Amurka ya bayyana sunan Shugaban babban bankin kasar Iran Waliyil...Saif a jerin mutune 4 da suka kakabawa takunkumi, baya ga wannan babban jami'in tattalin arzikin kasar Iran, an ambato wasu mutanan guda uku da suka hada da Ali Taraz Ali dan kasar Iran, da kuma Habib Karem na kasar Labnon da Muhamad Kasir shugaban Bankin Albilad na kasar Iraki.
A makon da ya gabata ma, Baitul malin kasar Amurkan ya kakabawa wasu mutane 6 tare da wasu kamfanoni uku na kasar Iran takunkumi.
A ranar 8 ga wannan wata na Mayu da muke ciki ne shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana ficewar kasarsa daga yarjejjeniyar nukiliyar Iran,duk da irin adawar da ya fuskanta da mafi yawa daga sanatocin Amurka da kawayenta na Turai.