Venezuela Ta Kori Manyan Jami'an Diflomatsiyan Amurka
(last modified Wed, 23 May 2018 05:51:17 GMT )
May 23, 2018 05:51 UTC
  • Venezuela Ta Kori Manyan Jami'an Diflomatsiyan Amurka

Shugaba kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya sanar da korar wasu manyan jami'an diflomatsiyan Amurka su guda biyu daga kasar, wanda suka hada da mai kula da harkokin Amurka a Karakas babban birnin kasar, wanda shi ne wani jami'in diflomatsiyan Amurka mafi girma.

Wannan matakin na Venezuela, ya biyo bayan da Amurka ta sanar da kakaba wasu sabbin jerin takunkumin tattalin arziki ga kasar ta Venezuela, bayan sanar da sake zaben Shugaba Maduro.

Mista Maduro ya ce ya baiwa jami'an na Amurka, wa'adin sa'o'i 48 na su fice daga kasar.

Da yake bayyana hakan a zauren majalisar tsare zabe ta kasar, shugaba Mduro ya yi watsi da duk takunkuman na Amurka, tare da dora alhakin dukkan wahalhalun da 'yan kasar ke sha ga Amurkar.  

Shugaba Maduro ya zargi jami'in diflomatsiyan dake kula da harkokin Amurka a Karakas, Robinson, da shirya makarkashiya a harkokin soji da neman ruguza tattalin arzikin kasar da kuma kiran kin kada kuri'a a zaben kasar na ranar Lahadi data gabata.