Ganawar Trump Da Kim Jong-un Ta Shiga Rashin Tabas
(last modified Wed, 23 May 2018 05:51:44 GMT )
May 23, 2018 05:51 UTC
  • Ganawar Trump Da Kim Jong-un Ta Shiga Rashin Tabas

Shugaba Donald Trump, na Amurka ya bayyana cewa, mai yiwa a daga ganawar da ya shirya zai yi da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a ranar 12 ga watan Yuni a Singapore

Wannan dai shi ne karo na farko da Trump, ya bayyana karara yiwuwar dage tattaunawar ta kud-da-kud daKim Jong Un, duk da cewar shi Trump din, shugaban na Koriya ta Arewa da gaske yake akan kwance shirin nukiliyar kasarsa.

Trump ya ce idan ganawar ta 12 ga watan Yuni ta cutura, za'a gudanar da ita a wani lokaci nan gaba, tare da gindaya wasu sharudda, wanda bai fayyace ba.

Wannan bayyanin dai ya fito ne a yayin ganawar da shugaban na AMurka ya yi da takwaransa na Koriya ta Kudu, Moon Jae-in, a jiya Talata a fadar White House.

Bayan ganawar shugabannin biyu, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya shaida wa masu aiko da rahotanni cewa, suna aiki tukuru don ganin ganawar ta 12 ga watan na Yuni mai zuwa ta wakana kuma a cikin nasara.