Faransa : Macron Ya Yi Kiran Zuba Jari A Rasha
Shugaba Emmanuel Macron, na Faransa ya yi kira ga kamfanonin kasarsa akan su kara zuba jari a Rasha, musamman a bangaren da suka fio karfi kamar abincin na safarawa da harkokin sarararin samaniya da kuma kayan lataroni.
Mista Macron ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da yake a Rasha a inda kuma yake halartar babban taron kasuwanci na hadin gwiwar kasashen Rasha da Faransa, a birnin Saint-Petersbourg.
A nasa bangare shugaba Putin ya shaida cewa, Faransa babbar abokiyar huldar Rasha ce, inda ya yaba da habakar cinikayar dake tsakanin kasashen biyu, wanda ya kai 16,5% a 2017, duk da a cewarsa yana kasa da harkokin kasuwancio da China, abokiyar huldar kasar Rashar ta farko.
Faransa dai nada kamfanoni da yawansu ya kai 500 a kasar Rasha wanda ke aiki a fanonin da suka hada da makamashi, masana'antu da harkokin kudi.
Daga cikin yarjejeniyoyi hamsin da kasashen biyu suka sanya wa hannu a yayin ziyarar ta Macron a Rasha, harda ta kamfanin Total wanda zai zuba jari na Dalar Amurka Bilyan 2,5 a harkar iskar Gaz.