Yarjejeniyar Nukiliyar Iran Na Taimaka Wa Tsaron Turai_Mogherini
May 29, 2018 11:20 UTC
Babbar jami'ar kula da harkokin kasashen ketare na kungiyar tarayya turai, Federica Mogherini ta bayyana cewa, batun nukiliyar Iran na shafar tsaron kungiyar, maimakon tattalin arziki.
Kungiyar EU ta kira taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobinta a jiya, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan janyewar Amurka, da kuma wasu batutuwan da suka shafi yankin musamman yanayin yankin Gaza da kuma na Siriya da dai sauransu.
Bayan taron, Federica Mogherini ta bayyana wa manema labarai cewa, idan babu yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, yanayin tsaron yanki da kungiyar EU zai shiga cikin mawuyacin hali.
Tags