Rasha Ba Ta Da Niyyar Komawa Cikin Kungiyar G7
Kasar Rasha, ta ce ba ta da wata niyyar komawa cikin kungiyar kasashe mafiya tattalin arzikin a duniya na G7, a halin yanzu.
Wannan dai na zuwa ne, bayan kiran da shugaba Donald Trump, na Amurka, ya yi na cewa ya kamata a mayar da kasar Rashar cikin kungiyar.
Da yake sanar da hakan, ministan harkokin wajen Rashar, Sergueï Lavrov, ya ce wannan ba shi gaban kasarsa, don kuwa Rashar a yanzu, ta fi mayar da hankali ne kan sauran harkokin hadin gwiwa na tsarin G20.
Mista Lavrov, ya kuma kara da cewa, Moscow bata taba neman dawowa ba cikin kungiyar ta G8, wacce ta koma G7 a yanzu, tun bayan dakatar da ita bayan mamaye yankin Krimiya a shekara 2014.
Gabanin taron kasashen na G7 na wannan karo da aka bude Jiya a birnin Quebec na kasar Canada, kasashen Biritaniya, Faransa da kuma Jamus sun jadadda matsayinsu na kin amuncewa da sake mayar da Rashar cikin kungiyar a halin yanzu.