Singapore : Kallo Ya Koma Kan Ganawar Trump Da Jung Un
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Singapore a daren jiya, don shirya halartar ganawa a tsakaninsa da shugaban kasar Koriya ta Arewa a ranar 12 ga wannan wata.
Bisa shirin da aka tsara, Trump da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai yi ganawa a otel na Capelle dake tsibirin Sentosa a ranar 12 ga wannan wata, wannan zai zama karo na farko da shugabannin Amurka da na kasar Koriya ta Arewa suka yi ganawa a tarihi.
Yau ne dai firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong zai gana da shugaba Trump, bayan da ya riga ya gana da Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da shi ma ya isa kasar Singapore.
Wannan ganawar dai idan ta wakana, zata kasance zakaren gwajin dafi akan anniyar Koriya ta Arewa akan kwance makamanta na nukiliya, a lokacin koriya ta Arewar ke cewa ba zata bada kai ga bori ya hau ba, muddun Amurka da Koriya ta Kudu na zaman babbar barazana gare ta.
Amurka dai na son Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na nukiliya da kwata kwata, da bada damar yin binkice