MDD Ta Amince Da Kudirin Goyon Bayan Al'ummar Palastinu
(last modified Thu, 14 Jun 2018 05:48:53 GMT )
Jun 14, 2018 05:48 UTC
  • MDD Ta Amince Da Kudirin Goyon Bayan Al'ummar Palastinu

A ci gaba da goyon al'ummar Palastinu, manbobin MDD sun amince da wani kudiri na yin alawadai da ta'addancin da yahudawan sahayoniya ke ci gaba da yi kan al'ummar Palastinu.

A jiya laraba ce Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taron gaggauwa domin yin nazari kan halin da yankin zirin gaza ke ciki, hakan kuwa na zuwa ne bayan da kasashen larabawa suka gabatar da wani kudiri na neman goyon bayan Duniya ga al'ummar Palastinu. 

Wannan kuduri ya samu amincewa da gagarimin rinyaje da kuri'u 120 a gaban kuru'u 45 da suka yi watsi da shi, sannan kuma kasar Amurka ta sha kayi kan wani kudiri da ta gabatar da yin alawadai da kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a kan halba makamai masu linzami zuwa haramtacciyar kasar Palastinu.

Nicky Haley wakiliyar Amurka a zauren MDD ta bayyana cewa a halin yanzu akwai rikici da dama a Duniya amma MDD ta fi karkata zuwa rikicin Palastinu tare kuma da yin alawdai da Haramtacciyar kasar Isra'ila.