Russia 2018 : Rasha Ta Lallassa Saudiyya 5-0
Rasha dake karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya 2018, ta lallasa Saudiyya da ci 5 da 0 a wasan bude gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya da aka yi a birnin Mosko.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya halarci wasan, wanda shi ne na farko da aka buga a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kasarsa ke karbar bakunci.
Dan wasan Rasha, Youri Gazinsky, shi ne ya fara zura kwallo a ragar tawagar kwallon kafa ta Saudiyya a mintuna 12 da soma wasan.
A ci gaban da wasan yau Juma'a za'a kara tsakanin Jamhuriya Musulinci ta Iran da kuma Morocco, a filin wasa na Saint-Pétersbourg.
Samun nasara a wasan na farko ga Iran ko Morocco nada matukar mahimmanci idan aka yi la'akari da rukunin B da suke ciki, wanda ya kunshi Spain da kuma Portigal, wandanda su ma zasu fafata da yammacin yau Juma'a a filin wasa na birnin Sotchi.
Haka kuma a yau Juma'a akwai karawa tsakanin Masar da Uruguay a filin wasa na birnin Ekaterinbourg, amma a rukunin A.