Matsalar Bakin Haure Tana Kara Raba Kan Kasashen Turai
Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa kasarsa ba zata iya karban dukkan bakin hauren da kasar Italia ta ware mata ba.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto shugaban Emmanuel Macaron yana fadara haka a jiya Alhamis a lokacinda sabani kan karban karin bakin haure tsakanin Faransa da Italia yake kara tsanani. Shugaban Macron , ya ce abin mamaki shi ne wasu wadanda baa sa da masaniya kan yawan kudaden da kasar Faransa za ta iya kashewa bakin haure ba suna kokarin nunawa kasar cewa sun san abinda ya dace.
Shugaban ya bada shawarar rufe wani bangare na kan iyakokin kasar da ma dakatar da ba batun bada mafaka ga bakin haure kwata-kwata a kasar, don gudan daukar nauyin da ba zata iya ba.
Kafin haka dai ministan cikin gida na kasar Italia ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa ta amshi bakin haure ne a madadin kasashen na Turai, don haka bai kamata kasashen su kyaleta bakin ba.
A makon da ya gabata ne kasar Italia ta ki karban wasu karin bakin haure da aka ceto daga halaka, wanda yasa kasar Faransa take ganin bata yi dai dai ba.