Rasha 2018: Nijeriya Ta Lallasa Kasar Iceland Da Ci 2-0
(last modified Fri, 22 Jun 2018 18:15:19 GMT )
Jun 22, 2018 18:15 UTC
  • Rasha 2018: Nijeriya Ta Lallasa Kasar Iceland Da Ci 2-0

A ci gaba da gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ake gudanarwa a kasar Rasha, kungiyoyin kwallon kafa na Nijeriya da Brazil sun sami nasarar lallasa abokan karawarsu na kasashen Iceland da Costa Rica da ci bibbiyu da nema.

A wasan da ta buga dazu dazun nan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Nigeria din ta sami nasarar lallasa abokiyar karawarta ta kasar Iceland da ci 2-0, lamarin da ya sake sanya fata cikin zukatan miliyoyin masoya kwallon kafa a Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka.

Nijeriyar wacce ta ke buga wasa a rukuni (group) na D ta sami nasarar sanya kwallayen nata ne ta hannun dan wasanta Ahmad Musa a mintuna na 49 da 75 lamarin da ya ba wa Nijeriya din damar zama na biyu a rukunin na su da ke dauke da kasashen Croatia da take a matsayi na 1 da maki 6, sai Nijeriya na biyu da maki 3 sai kasar kasashen Iceland da Argentina da suke a matsayi na uku da na hudu.

Wasan karshe da Nijeriya za ta buga dai za ta buga shi da kasar Argentina.

Kafin wasan Nijeriya din an buga wasa tsakanin kasashen Brazil da Costa Rica, inda Brazil din ta sami nasara da ci 2-0.

A halin yanzu kuma ana ci gaba da wasa na uku na yau din tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Swiss da Serbia, inda kafin shigowarmu dakin wasa labarai, Serbia tana da ci 1- Swiss kuma tana nema.