Shugaba Asad Ya Ce Tattaunawa Da Amurka Bata Lokaci Ne Kawai
(last modified Sat, 23 Jun 2018 11:15:12 GMT )
Jun 23, 2018 11:15 UTC
  • Shugaba Asad Ya Ce Tattaunawa Da Amurka Bata Lokaci Ne Kawai

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya ce ba ya jin akwai bukatar kokarin neman tattaunawa da gwamnatin Donald Trump ta Amurka don cimma wata matsaya ta magance rikicin da ke faruwa a kasarsa yana mai bayyana hakan a matsayin bata lokaci kawai.

Shugaba Assad ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin kasar Rasha inda ya ce tattaunawa da Amurka a halin yanzu babu wani abin da zai haifar, kawai bata lokaci ne. Don haka ba za mu taba tattaunawa da Amurkawa wai a matsayinsu na Amurkawa ba, yana mai cewa kasar Siriyan a shirye ta ke ta tattaunawa da kowane mutum matukar dai hakan zai haifar da wani sakamako mai kyau.

A wani bangare na hira, shugaban na Siriya ya ce matsalar shugabannin Amurka ita ce cewa suna gudanar da siyasarsu ne karkashin irin tasiri da tursasawan da suke fuskanta daga cibiyoyi na kudi da masu kare manufofin wasu mutane da suke Amurka, don haka ne ba za iya tabuka komai sai abin da wadancan mutanen suke so.

Gwamnatin Siriyan dai tana zargin Amurka da wasu kasashen Yammaci da goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda da suke ci gaba da yaki a kasar Siriya.