Kofin Duniya:Koriya Ta Yi Waje Da Jamus
(last modified Wed, 27 Jun 2018 19:03:41 GMT )
Jun 27, 2018 19:03 UTC
  • Kofin Duniya:Koriya Ta Yi Waje Da Jamus

A Ci gaba da fafatawar da aka yi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya Koriya ta Kudu ta doke Jamus da ci 2-0 a karawar da suka yi da yammacin nan.

Tawagar kwallon kafar Koriya ta Kudu ta yi waje da Jamus mai rike da kambo a gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Rasha.

Wannan na zuwa ne bayan Koriya ta zura kwallaye biyu a ragar Jamus a dai dai lokacin da ake shirin tashi na wasan wanda suka fafata a Kazan.

Korea ta Kudu ta jefa kwallaye biyu a mintina na 92 da 96, bayan an kara wa kasashen biyu lokaci bayan kwashe minti 90 ba tare da zura kwallo ko guda ba.

A karon farko a tarihin kwallon kafa na duniya an fidda Jamus a zagayen farko na gasar,tarihi ya nuna rabon da a kori Jamus a irin wannan yanayi tun a shekarar 1938.

Jamus wadda ita ce ke rike da kofin a yanzu ta sami nasarar daukar kofin kwallon kafar na duniya har sau hudu a bayas,sai dai duk da nasarar da Koriya ta Kudu ta samu ba za ta iya wucewa zuwa zagaye na gaba ba.