Rasha: Barazanar Ayyukan Ta'addanci A Cibiyoyon Kasuwanci 3 A Garin Samara
(last modified Fri, 29 Jun 2018 06:45:00 GMT )
Jun 29, 2018 06:45 UTC
  • Rasha: Barazanar Ayyukan Ta'addanci A Cibiyoyon Kasuwanci 3 A Garin Samara

Gine-ginen cibiyoyin kasuwanci guda ukku ne mutane suka fice daga cikinsu baya an sami sakon barazanar ta'addanci a wuraren.

Majiyar muryar JMI ta nakalto cewa gine-ginen cibiyar kasuwanci ukku ne mutane suka kaurarcewa sanadiyar karban sakon barazanat dasa boma-bamai a cikinsu a garin Samara daya daga cikin garuruwan da ake gudanar da gasar gwallon kafa ta duniya a halin yanzu a kasar Rasha.

Labarin ya kara da cewa tun farkon watan Satumban shekara ta 2017 , ya zuwa yanzu mutane kimani dubu 7000 suka kauracewa wasu gine-gine na kasuwanci ko na jama'a don samun sakon barazanan ayyukan ta'addanci a kasar Rasha. 

Jami'an tsaron Rasha sun bayyana cewa wayoyin da ake amfani da su wajen aika da sakonnin barazanar da su duk na kasashen waje ne.