EU Ta Jadadda Takunkumin Da Ta Kakabawa Rasha
(last modified Fri, 29 Jun 2018 11:45:17 GMT )
Jun 29, 2018 11:45 UTC
  • EU Ta Jadadda Takunkumin Da Ta Kakabawa Rasha

Kungiyar tarayyar Turai ta sake jadadda takunkumin da ta kakabawa kasar Rasha na tsahon watani shida

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa kasashen Turai 28 sun amince da jadadda takunkumin da suka kakabawa kasar Rasha na tsahon watani 6 a zaman da suka yi jiya alhamis a birnin Brussels.

Wannan takunkumi ya shafi wani bangare na tattalin arzikin kasar Rasha daga ciki harda cinikayar Man fetir.

Wani jami'i na kungiyar tarayar turai da ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bayan dogon bahasi kan mas'alar kasar Ukreine da yarjejjeniyar da aka cimma ta Minisk.

A karshen shekarar 2014 ne aka cimma yarjejjeniyar sulhu ta Minisk tsakanin gwamnatin Ukrene da 'yan tawayen gabashin kasar bisa shiga tsakanin kungiyar tarayyar Turai da goyon bayan kasar Rasha, sannan a shekarar 2015 an sake wannan zama, to saidai daga baya bangarorin biyu suka kafa suka shure wannan yarjejjeniya.