Kasashen Turai Sun Cimma Matsaya Kan Mayar da 'Yan Gudun Hijra
Gwamnatin kasar Jamus ta sanar da cewa kasashe 14 manbobin kungiyar tarayar Turai sun cimma matsaya kan yadda za a mayar da 'yan gudun hijra kasashen da suka fara neman mafuka
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta sanar da kasashe 14 ciki harda kasashen da a baya suka bayyana adaswarsu da siyasar karbar bakin haure, da cewa sun cimma matsaya na karbar 'yan gudun hijrar da suka nemi mafuka a kasashen a baya.
Wannan yarjejjeniya ta ceto gwamnatin hadakar kasar jamus daga wargajewa, bayan da ta fuskanci matsin lamba daga abokinin hadakarta kan mayar da 'yan gudun hijrar zuwa kasashen da suka fito .
Daman a watan gobe ne wa'adin da aka bai wa Merkel ke cika kan samar da mafita ko kuma ta fuskanci barazanar rushewar gwamnatin hadakar da aka kafa bayan da a ka kwashi dogon lokaci ana kai ruwa rana.
Yanzu za a soma mayar da 'yan gudun hijirar da suka shigo kasar daga wata kasar Turai, cibiyar da aka tanadar musu a yayin da Jamus ke ci gaba da duba cancartasu na zama a kasar.
Tuni dai Merkel ta mika sakamakon wannan yarjejeniyar da ta cimma da wasu kasashen yankin goma sha hudu a gaban jagororin jam'iyyun hadakar. A zaman taron na jiya Juma'a na birnin Brussels an yarda a samar da wasu cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira a wasu kasashen da ba na Turai ba.