Dan Takara Ra'ayin Sauyi Ya Lashe Zaben Mexico
A Mexico, dan takarar masu ra'ayin kawo sauyi, Andres Manuel Lopez Obrador, ya lashe zaben shugaban kasar, wannan shi ne karon farko da wani dan takara mai wannan ra'ayin ya lashe zaben wannan kasa.
Mista Obrador, ya lashe zaben ne da kashi kusan 54% na yawan kuri'un da aka kada, a yayin da dan takara jam’iyyar masu ra’ayin rikau Ricardo Anaya, ya samu kashi 22%, kamar shugaban hukumar zaben kasar Lorenzo Cordova ya sanar.
Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Mista Obrador, ya yi wa 'yan kasar alkawarin kawo sauye sauye, musammam a fanin yaki da cin hanci da rashawa, da matsalar 'yan fataucin muggan kwayoyi.
Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump, wanda dangantakarsa da shugaban Mexico mai barin gado, ya taya sabon shugaban kasar Murna akan nasara lashe zaben.