Jul 11, 2018 17:51 UTC
  • Merkel Da Trump Sun Yi Musayar Zafafen Kalamai A Taron NATO

Gwamnatin Jamus ta mayar da martani kan kalaman shugaba Donald Trump na Amurka, na cewa kasar ta Jamus ta zamo ''yar amshin shatan Rasha'', tare da bukatar kasar ta Jamus da ta gaggauta inganta sha’anin tsaronta a maimakon dogaro da Rashar.

A yayin da isa a Brussuls, inda take halartar taron kungiyar NATO, shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta maida martanin cewa ''Jamus kasa ce mai 'yancin kanta, dake yanke shawara da kanta''

Masana dai na kallon taron kwanaki biyu na kungiyar tsaro ta NATO da ke gudana a birnin Brussels, a matsayin mafi zafi da ba a taba ganin irinsa a cikin tsawon shekaru.

A taron na bana dai kungiyar Tarayyar Turai da Amurka sun yi ta musayar zazzafan kalamai marar dadi, yayin da shugaba Trump ya bukaci sauran kasashen NATO da su linka kudaden samar da tsaro dake suke bayar wa a kungiyar ta NATO.

Wannan taron na NATO na zuwa ne a yayin da ya rage kasa da mako guda shugaba Trump ya yi ganawarsa ta farko da shugaban Rasha, Vladimir Putin a birnin Heksinki.

Tags