EU Ta Ce Bata Amince Da Mamayar Yankunan Palasdinawa Ba
Kakakin Babbar jami'a mai kula da harkokin kasashen waje na kungiyar tarayyar Turai ya bayyana cewa kungiyar bata amince da mamayar da HKI take wa yankunan Palasdinawa na bayan yakin shekara ta 1967 ba.
Tashar talabijin ta Rusiyal-Yaum ta kasar Rasha ta nakalto Maya Kutsianchic mai magana da yawun Federica Mogrini , Jami'a mai kula da lamuran harkokin waje na tarayyar Turai yana fadar haka a jiya Jumma'a.
Maya Kutsianchic ya kara da cewa kungiyar ta EU tana bin labaran abinda ke faruwa a kasar Iceland inda majalisar dokokin kasar ta kafa dokar hana shigo da kayakin da aka yi a kasar Isara'ila musamman a yankin yamma da kogin jordan da kuma sauran yankunan da HKI ta mamaye bayan yakin shekara ta 1967.
A ranar laraba da ta gabata ce majalisar dattawan kasar Iceland ta amince da wata doka wacce ta haramta saya ko kuma shigo da kayakin kamfanonin HKI wadanda aka kera su a yankunan da HKI ta mamaye wadanda suka hada da yammada da kogin jordan ba birnin Quds. Majalisar ta Icelanda ta dauki wannan marakin ne don nuna goyon bayanta ga al-ummar Palasdinu .
Wannan matakin dai ya fusata yahuadawan HKI sai dai babu abinda zasu iya don yadda zaluncin da suke wa al-ummar Palasdina yake kara yaduawa a duniya.