Kasar Italiya Ta Karbi 'Yan Gudun Hijra Na Kasashen Afirka
Gwamnatin Italiya ta amince da bai wa daruruwan 'yan gudun hijira da suka fito daga Afirka mafaka bayan da ta sami amincewar kungiyar kasashen Turai ta EU kan rarraba su a tsakanin sauran kasashe mambobinta.
A wannan Litinin ce kasar Italiya ta amince da karbar dariruwan 'yan gudun hijrar da suka fito daga kasashen Afirka, bayan da ta samu lamini daga sauran kasashen Turan na cewa za a rarraba su a tsakanin kasashen.
A baya dai gwamnatin Italiyan taki amincewar da karbar 'yan gudun hijrar, inda suka kwashe kwanaki cikin rinjin ruwa a gabar ruwan na Italiya.
Wannan lamarin ya kawo karshen halin wahalar da daruruwan 'yan gudun hijirar suka tsinci kansu a kwanakin da suka kwashe suna zaune cikin kwalekwale a gabar ruwan kasar bayan da suka baro kasashensu na asali.
Kasashen mambobi a kungiyar tarayyar Turai sun amince da su karbi fiye da rabin 'yan gudun hijirar, a yunkurin dinke barakar da aka samu a tsakanin kasashen na mayar da 'yan guun hijrar zuwa kasashen Afirka.
Dokokin kasa da kasa dai ta haramta mayar da 'yan gudun hijirar da suka tsere daga rigingimu masu hadari ga rayuwarsu kasashensu na asali.