Amurka Ta Hana Wa Tawagar Falasdinawa Visa
Jakadan Palasdinu, a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansur, ya bayyana cewa Amurka ta hana wa wata tawagar Palasdinun takardar Visa ta shiga Amurka, domin halartar wani taron MDD a birnin New York.
Kamar sauren mambobin Majalisar Dinkin Duniya, an tsara iat ma Palasdinun za ta gabatar da rahotonta kan kokarin da take na cimma maradun karni na MDD da ake son cimma wa kafin nan da shekara 2030.
Dangantaka tsakanin Amurka da Palasdinu dai ta yi tsami, tun bayan da Amurka ta ayyana Qudus a matsayin babban birnin yahudawan mamaya na Isra'ila a karshen shekara 2017 data gabata, kuma tun lokacin ne Palasdinawa suka ware Amurka daga duk wani shirin samar da zaman lafiya tsakaninsu da Isra'ilar.
Babu dai wani karin bayyani daga bangaren wadanda suka shirya taron, dama Amurkar da kuma MDD.
Wakilin Palasdinawa mai kujerar 'yan sa ido a MDD, ya bayyana cewa zai bi hanyoyin da suka dace don shigar da kara a gaban MDD.