Faransa Da Rasha Zasu Bada Kayan Agaji Ga Siriya
(last modified Sat, 21 Jul 2018 05:47:48 GMT )
Jul 21, 2018 05:47 UTC
  • Faransa Da Rasha Zasu Bada Kayan Agaji Ga Siriya

Kasashen Faransa da Rasha sun cimma wata matsaya ta aike wa da kayan agaji a yankin Ghouta dake yammacin Siriya, wanda sojojin gwamnatin Bashar Al'assad suka kwato a watan Afrilu da ya gabata.

Wannan shirin dai a cewar sanarwar hadin guiwa ta kasashen biyu, zai taimaka wa wajen isar da kayan agaji ga fararen hula, kamar yadda kudirin kwamitin tsaro na MDD, mai lamba 2401 ya tanada.

Jirgin dakon kayan da Rasha ta tura a Faransa zai kwaso kayan agaji da yawansu ya kai ton hamsin, domin isar dasu a yammacin kasar ta Siriya a cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar.

Wannan shi ne tallafin hadin gwiwa irinsa na farko na tsakanin Faransa da Rashar wacce ta yi gaban kanta domin taimaka wa gwamnatin Bashar Assad a shekara 2015.

A wannan Asabar ce ake sa ran ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, (OCHA), zai fara raba kayan agajin.