An Cabke Wani Masanin Kera Makami Mai Linzami A Rasha
Wani masanin kera makami mai linzami dan kasar Rasha mai shekaru 74 ya shiga hanu kan laifin cin amanar kasa
Tashar talabijin din kasar Rasha ta habarta cewa a wannan Lahadi wata kotu a birnin Moscow ta bayar da umarnin tsare Victor Kudryavtsev gungu a cibiyar bincike na kera motoci a Rasha kuma shugaban cibiyar masu tsara yadda ake kera makami mai Linzami, bayan da ta same shi laifin fitar da fusahar kasar zuwa kasashen ketara, wanda hakan na a matsayin cin amanar kasa.
Tuni dai jami'an tsaro suka cabke wannan mutum, inda kuma suka fara gudanar da bincike a ofishinsa dake jami'ar Lefortovo ta kasar Rasha.
A ranar juma'ar da ta gabata ce kafafen yada labaran kasar Rasha suka sanar da cewa an fitar da sirrin kera makami mai Linzami na kasar Zuwa kasashen ketare, kuma wannan sirri ya fita ne daga cibiyar bincike na kera motoci a kasar, inda tuni ma'aikatar tsaron kasar ta fara gudanar da bincike domin gano hakikanin lamarin.