Turkiya Ta Bude Ofishin Jakadancinta A Afirka Ta Kudu
(last modified Thu, 26 Jul 2018 19:07:51 GMT )
Jul 26, 2018 19:07 UTC
  • Turkiya Ta Bude Ofishin Jakadancinta A Afirka Ta Kudu

A yayin buda ofishin jakdancin kasar Turkiya a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu, ministan harakokin wajen Turkiya ya bayyana shirin kasar na kara yawan ofishin jakadancin kasar a kasashen Afirka

Kamfanin dillancin labarai na Anatolia ya nakalto Mevlüt Çavuşoğlu ministan harakokin wajen Turkiya a wannan alhamis yayin buda ofishin jakadancin kasar a birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu na cewa, a halin da ake cikin kasarsa nada ofishin jakadanci ko karamin ofishin jakadanci 241 a Duniya, kuma a halin yanzu kasarsa na shirye shiryen karin yawan ofishin jakadanci daga 41 zuwa 50 a kasashen Afirka.

Mevlüt Çavuşoğlu ya ce domin gudanar da harakokin kasuwanci a matakin kasa da kasa, Turkiya na bukatar ta kasance a ko wani lungu na Duniya.

Mevlüt Çavuşoğlu ministan harakokin wajen kasar Turkiya da Shugaban kasar Rajab tayyib Ordugan sun ziyarci kasar Afirka ta kudu, inda suka gana da hukumomin kasar.