MDD ta bukaci 'yan siyasar Zimbabwe su kai zuciya nesa
(last modified Thu, 02 Aug 2018 11:50:46 GMT )
Aug 02, 2018 11:50 UTC
  • MDD ta bukaci  'yan siyasar Zimbabwe su kai zuciya nesa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci bangarorin siyasar Zimbabwe da su kai zuciya nesa, biyo bayan tarzomar da ta barke a kasar saboda zargin magudin zabe.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Sakatare janar na MDD Antonio Guterres na cewa muna kira da shugabanin 'yan siyasa da kuma al'ummar kasar Zimbabwe suka zuciya nesa, su kauracewa tashin hankali har lokacin da za a warware sabanin da ya kunno kai da kuma bayyana sakamakon zabe na karshe.

Guterres ya bukaci bangaren gwamnati da 'yan adawa su kiri zaman lafiya, su kuma kaucewa tashin hankali a kasar.

Ya zuwa yanzu dai wannan tarzomar bayan zabe, wacce ta faro daga gudanar da zanga-zanga tayi sanadiyar asarar rayukan mutane 3.

ta kuwa kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta bukaci gwamnatin Zimbabawe da ta kaddamar da bincike kan matakan da sojoji suka dauka na amfani da karfin da ya wuce kima wajen kai hari kan masu zanga zanga.