An Cabke Wasu Rashawa A Amurka
'Yan Sandar Amurka sun cabke wasu 'yan kasar Rasha 4 a yankuna daban daban na kasar
Tashar Talabijin din Rusiya Alyaum ta nakalto karamin jakadan kasar Rasha a birnin New York na cewa 'yan sandar Amurka sun kame 'yan kasar Rasha 4 bisa zargin amfanin da kudin ganye.
Rahoton ya cewa an kame 'yan kasar Rasha biyu ne a birnin Los Angeles, yayin da aka kame guda a birnin New York, na hudun kuma ba a bayyana inda aka kame shi ba.
Karamin jakadan kasar Rasha ya yi watsi da tuhumar da ake yiwa 'yan kasarsa, sannan ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Kafin hakan dai jami'an tsaron Amurka sun kame Maria Batina mai shekaru 29 da haifuwa 'yan kasar Rashan a kasar Amurka bisa zargin leken asiri.
A Shekarun baya-bayan nan sabani tsakanin kasashen Rasha da Amurka na kara karuwa, musaman ma bayan rikicin kasar Ukrene da kuma bayan zaben Amurka, inda 'yan kasashen biyu ke fuskantar kame-kame daga bangarorin biyu.