Amurka Zata Dorawa Rasha Sabbin Takunkuman TattalinArziki.
(last modified Thu, 09 Aug 2018 06:56:02 GMT )
Aug 09, 2018 06:56 UTC
  • Amurka Zata Dorawa Rasha Sabbin Takunkuman TattalinArziki.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa zata kakabawa kasar Rasha sabbin takunkuman tattalin arziki saboda zargin ta yi amfani da iska mai guba wajen halaka Sergei Skripal a kasar Britania.

Sergei Skripal dai tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin kasar Rasha wanda yake zauni a birnin Salisbury na kasar Britania, wanda kuma a cikin watan Maris da ya gabata ne aka yi amfani da iska mai guma aka kashe shi tare da diyar.

Gwamnatin kasar Brirania tana tuhumar kasar Rasha da hannu wajen kissan mutumin, amma gwamnatin kasar Rasha ta musanta hakan. Da wannan dalilin ne gwamnatin kasar Britania ta kori jami'an diblomasiyyar kasar Rasha 23 daga kasar, a yayinda kasar Rasha ta maida martani da korar jami'an diblomasiyyar 23 na kasar Britania daga Rasha.

Kamfanin dillancin labaran Ruters ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka, don nuna goyon bayanta ga kasar Britania a jiya Laraba ta bada sanarwan cewa zata kakabawa kasar Rasha takunkumi a ranar 22 ga watan Augustan da muke ciki sanadiyyar kisan Srgei Skripal.