Kasar Indiya Ta Ki Ba Wa Limamin Makka Izinin Shiga Kasar
(last modified Sat, 02 Apr 2016 04:48:40 GMT )
Apr 02, 2016 04:48 UTC
  • Kasar Indiya Ta Ki Ba Wa Limamin Makka Izinin Shiga Kasar

Ofishin jakadancin kasar Indiya a birnin Riyadh na kasar Saudiyya ya ki ba wa limamin masallacin Masjid al-Haram kana kuma daya daga cikin masu wa'azin wayabiyawa mai tsaurin ra'ayi Sheikh Saleh al-Taleb takardar izinin shiga kasar saboda gudun abin da zai iya zuwa ya komo.

A wani labari da ta buga a shafinta na Internet tashar talabijin din Al-Alam da ke watsa shirye-shiryenta cikin harshen larabci daga Iran ta nakalto jaridar The Times of Indiya tana cewa: Sakamakon hana Sheikh Saleh al-Taleb takardar izinin shiga kasar Indiya, an soke wani biki da aka shirya yi inda aka tsara shehin malamin zai jagoranci sallar Juma'a a jiya a shataletalen Ghandi da ke garin Bahar na kasar Indiyan.

Wasu majiyoyi dai sun bayyana cewar dalilin da ya sanya gwamnatin Indiyan daukar wannan matsayi na hana ba wa malamin wahabiyan takardar izinin shiga kasar, duk kuwa da cewa an gayyace shi ne wani taro da masu shirya shi suka ba shi suna taron tattabar da zaman lafiya, hakan yana da alaka da tsoron da mahukutan Indiyan suke da shi ne na yiyuwar kai wa malamin wahabiyan hari kamar yadda aka kai wa Sheikh A'idh al-Qarni, shi ma wani shehin malamin wahabiyawan da aka kai masa hari a kasar Indiyan a baya.

Kasashen duniya da dama dai suna ci gaba da nuna damuwarsu dangane da irin yadda akidar Saudiyya ta wahabiyanci yake yaduwa a duniya sakamakon alakar da yake da ita da ayyukan ta'addanci da tsaurin ra'ayin addini da ke faruwa a duniya.