Tsohon Dan Majalisar Dattijai Ya Zargi Amurka Da Kirkiro Da'esh
Tsahon dan majalisar dattijan na Amurka -Kelly Ward daga Arizona ya ce: Tsoffin shugabannin Amurka suna da hannu wajen kirkiro kungiyar Da'esh.
Ward ya ce tsohon shugaban kasar Barrack Obama da tsohuwar ministar harkokin waje Hillary Clinton da kuma John MacCain sun taka rawa wajen kirkirar kungiyar ta 'yan ta'adda.
Ward ya kara da cewa; A 2011 MacCain ya bukaci ba da makamai ga kungiyoyin kasar Libya masu adawa da Khaddafi, wadanda bayan shekaru 4 su ka kashe jakadan Amurka a Libyan.
Ward ya kuma ce; Bayan wannan lokacin John MacCain da Clinto da Obama sun mayar da kasar Libya ta zama wata tunga ta 'yan ta'adda.
Tsohon dan majalisar dattijan na Amurka ya ce gabanin mutuwar John MacCain ya bukaci a bai wa 'yan ta'addar kasar Syria kudaden da su ka kai dala biliyan daya da miliyan 300 domin sayen makamai.