Rasha Tana Goyon Bayan Kasar Syria Domin Fada Da Ta'addanci
(last modified Fri, 07 Sep 2018 06:30:15 GMT )
Sep 07, 2018 06:30 UTC
  • Rasha Tana Goyon Bayan Kasar Syria Domin Fada Da Ta'addanci

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bakin kakakinta Maria Zakharova ce ta bayyana cewa kasar tana ba da cikakken goyon baya ga gwamnatin Syria a yakin da take yi da 'yan ta'adda

Zakharova ta kara da cewa; Sojan saman kasar Rasha da suke a yankin Idlib suna aiki ne kafada da kafada da sojojin Syria domin rusa dukkanin sansanonin 'yan ta'adda da ke yankin.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta zargi 'yan ta'adda da kai wa fararen hula hare-hare.

Bugu da kari Zakharova ta ce kyale 'yan ta'adda a yankin Idlib har zuwa wani lokaci mai tsawo ba abu ne da za a lamunta da shi ba.

Rasha da kawayenta sun sha alwashin tsarkake yankin Idlib daga mamayar 'yan ta'adda, musamman kungiyoyin Da'esh da kuma Nusrah.